22 Agusta 2020 - 10:49
Sayyid Huthy: Amurka Da HKI Suna Sarrafa Larabawa Masu Kulla Alaka Da Su Yadda Suke So

Shugaban kungiyar “Ansarullah” ta kasar Yemen, Sayyid Abdulmalik Badruddin al-Huthy wanda ya gabatar da jawabi dangane da shigowar sabuwar shekarar musulunci a jiya Alhamis ya bayyana cewa; Gwamnatocin Saudiyya, Hadaddiyar Daular Laraba, da Bahrain ba abinda ya hada su da zaman lafita, domin duniya tana ganin yadda su ke cutar da al’ummunsu.

ABNA24 : Sayyid Abdulmalik al-Huthy ya ci gaba da cewa; Kasashen da su ke yin biyayya ga HKI suna adawa da duk wanda yake fada da ‘Yan sahayoniya, don haka ne muke ganin yadda Saudiyya take kama Palasdinawa da tsare su da kuma azabtar da su.

Shugaban kungiyar ta “Ansarullah” ya ci gaba da cewa; Kasashen larabawan da suke nuna kansu a matsayin abokan HKI su ne masu hana al’umma ci gaba saboda suna damfarawa mutane manufar da ba tad a wani amfani.

Har ila yau, Abdulalik al-Huthy ta bayyana cikakken goyon bayansa ga gwagwarmayar Hizbullah ta kasar Lebanon wacce ya kara da cewa; tana fuskantar makirce-makirce masu girma.

342/